Nigeria za ta fara amfani da maganin Ebola

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana ci gaba da nuna fargaba kan barkewar Ebola a kasar

Hukumomin lafiya a Najeriya sun cimma wata yarjejeniya da wani kwararre a fannin kimiyyar harhada magunguna da zai samar da wani magani, Nano Sylver domin yi wa mutanen da ke fama da cutar Ebola magani a kasar.

Sai dai Ministan lafiya na kasar, Farfesa Onyebuchi Chukwu bai yi karin haske ba game da kasar da ta yi maganin, kuma wanene dan Najeriyar da zai samar da magungunan da ba a taba jarabashi a kan dan adam ba.

Hukumomin sun sanar da hakan ne kwanaki kadan bayan hukumar lafiya ta duniya ta ce babu laifi ayi amfani da magungunan da ba a taba gwada su a kan bil'adama ba, don yi wa masu cutar Ebola magani a yammacin Afrika.

Farfesa Onyebuchi Chukwu ya jaddada cewa kawo yanzu mutane 11 ne suka kamu da cutar Ebola, kuma uku daga ciki sun mutu wadanda suka hada da dan Liberiyan nan da ya kai cutar kasar, Patrick Sawyer.