'Kungiyar IS na yiwa Burtaniya barazana'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Burtaniya ta damu game da masu kaifin kishin Islama a duniya

David Cameron yayi gargadin cewa mayakan Islama ka iya yin karfin da zasu iya kaiwa jama'a hari akan titunan Burtaniya matukar ba a dauki mataki ba.

A wani rubutu da yayi a jaridar Telegraph Firai Ministan ya ce martanin da ake mayarwa wajen kai agaji ga wadanda aikace aikacen kungiyar IS ya shafa bai wadatar ba, kuma ana bukatar wani kwakwaran martani na tsaro.

Wannan na zuwa ne yayinda shugabannnin choci suka bayyana damuwa game da yadda burtaniyan take tunkarar masu kaifin kishin Islama.

Kungiyar IS dai ta kwace wasu bangarorin arewacin Iraqi da kuma Syria

A cikin rubutun nasa Mr. Cameron ya ce za'a iya cimma burin samar da tsaro na gaskiya ne idan har aka yi amfani da dukkanin abinda ake bukata kama daga kudi da tallafi da diplomaciya domin taimkawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.