Kamaru ta rufe iyakarta da Najeriya

Hakkin mallakar hoto

Kasar Kamaru ta ce ta rufe iykarta da Najeriya domin gudun yaduwar Ebola.

A wata hira ta musanman da sashen Hausa na BBC, Ministan sadarwan kasar, kuma kakakin gwamnati, Issa Tchiroma Bakari ya ce matakin ya zama dole, ganin cewa cutar ta Ebola bata da magani.

Ya ce: "Najeriya ita ce kawa mafi muhimmnaci garemu ta fuskar kasuwanci. Kuma ko ita ma gwmanatin Najeriya ta dauki matakan takaita yaduwar cuta mai kisa. Mun dauki matakin ne don kare jama'ar mu."

Ministan ya kuma ce matakin zai shafi zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya zuwa Kamaru.

Sai dai ministan ya ce wannan matakin da suka dauke na dan wani lokaci ne kawai.

Najeriya dai na daga cikin kasashen yammacin Afrika da ake fama da Ebola.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane hudu a kasar.

Wadanda suka mutu a yammacin Afrika zasu kai dubu daya a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.