Ebola: Sawyer ya yi ganganci - Sirleaf

Hakkin mallakar hoto science photo library
Image caption Tun a shekarar 1976 aka gano kwayar cutar Ebola

Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf ta shaida wa sashen turanci na BBC cewa an ware dala miliyan biyar domin yaki da cutar annobar Ebola a kasar.

A baya kungiyoyin fararen hula sun bai wa kasar tallafin dala miliyan 20 domin yaki da cutar.

Game da batun Patrick Sawyer, mutumin da ya fara shigar da cutar Najeriya, Ellen ta kwatanta lamarin a matsayin abin takaici inda ta kara da cewa ya yi ganganci da nuna rashin sanin ya kamata.

Tun bayan zuwan Mr Sawyer Najeriya, ya zuwa yanzu mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin da ake kula da wasu da dama da suka kamu da cutar.

Annobar cutar ta Ebola wacce ta barke a baya bayannan daga kasar Guinea ta lakume rayuka sama da dubu bayan bazuwa da ta yi a Saliyo da Liberia da kuma Najeriya.