Wata ta warke daga Ebola a Najeriya

Ebola Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da warkewar daya daga cikin mutanen da su ka harbu da cutar Ebola a kasar.

Matar likita ce dake cikin wadanda ake yiwa magani a kasar saboda cutar.

Ta kasance ta farko da ta warke daga cutar ta Ebola a Naijeriya.

Ita wannan likita na daga ciki jami'an kiwon lafiya da suka duba dan kasar Laberiyan nan wanda cutar ta Ebola ta kashe bayan shigowar sa Naijeriya.

Dokta Nasiru Sani Gwarzo daya daga manyan jami'an cibiyar yaki da cutuka ta Nijeriya ya ce "lamarin abun farin ciki ne dake basu kwarin gwiwa."

Najeriya dai na daga cikin kasashen yammacin Afrika da ake fama da Ebola.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane hudu a kasar.

Wadanda suka mutu a yammacin Afrika zasu kai dubu daya a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

Karin bayani