Premier: za a hana saka bidiyon bogi

Hakkin mallakar hoto ThinkStock
Image caption Hotunan bidiyo na bogi kan yadu a intanet tun kamin tashashin talabijin su maimaita wasa

Hukumar dake shirya gasar Premier ta Ingila, ta ce za ta yi dirar mikiya akan magoya bayan kungiyoyin kwallo kafa masu saka hotonan bidiyo na bogi na cin kwallo a intanet.

A cewar hukumar wasu da dama sun saka irin wadannan hotuna a lokacin gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil, akwai kuma yuwuwar za a ci gaba da aikata hakan yayin da ake shirin fara gasar Premier ranar Asabar.

Sai dai hukumar ta yi gargadin cewa yin hakan ya sabawa dokar nan da take hukunta masu satar fasaha.

Yanzu haka samun hotunan bidiyo da ba a fitar da su a hukumance ba ya zama ruwan dare.

Mutanen da ke hakan na amfani ne da fasahar da ta saukaka tsayarwa ko kuma dawo da wasa baya yayin da ake watsa shi kai tsaye ta talabijin.

Hakan kuma yana bayar da damar masu mu'amulla da intanet su aika da hotunan bidiyon cikin dan kankanin lokaci.

Sai dai da yawa daga cikin masoya kwallon kafa ba su san cewa hakan da suke yi, suna keta dokar nan da ta hana satar fasaha ba ne.

Yanzu haka Darektan sadarwa na gasar Premier Dan Johnson ya ce suna shirin daukar matakin hana aukuwar hakan saboda tashoshin talabijin na biyan makudan kudade domin neman iznin nuna wadannan wasanni.

A cewar Johnson suna aiki kafada da kafada da kamfanin Twitter domin neman hanyar magance wannan matsala.