An hallaka Yazidawa 80 a Iraki

Hoshyar Zebari Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ministan harkokin wajen Iraki

Ministan harkokin wajen Iraki mai barin gado, Hoshyar Zebari ya bada karin haske kan kisan da wasu mayakan kungiyar ISIS suka yi ma wasu Yazidawa maza su tamanin a wani kauye dake arewacin kasar.Mr Zebarin ya ce an kasa mazajen rukuni biyu ne kana aka kashe su, aka kuma bar gawarwarkinsu yashe akan tituna.

Mr Zebari ya ce mai yiwuwa an kai hari a kan kauyen na Kawju ne domin ramuwar gayya kan harin da jirgin saman Amurka maras matuki ya kai.

Daga bisani Amurka ta ce hare haren da jiragen nata marasa matuka suka kai sun ragargaza wasu motoci biyu masu sulke na mayakan.

Ma'ailkatar tsaro ta Pentagon ta ce an lalata motocin a wani hari ta sama data kai

Karin bayani