An kashe yazidawa 80 a Iraki

Yan gudun hijira mabiya adinin Yazidis Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Yan gudun hijira mabiya adinin Yazidis

Hedikwatar tsaron Amurka, ta ce hare-haren da jiragen yakin Amurka marassa matuka da ake sarrafa su daga doron kasa suka kai, sun lalata wasu motocin yaki biyu a kusa da garin Sinjar da ke arewacin Iraqi.

A sanarwar da hedikwatar ta bayar ta ce, an kai hare-haren ne bayan rahotannin da ke cewa, mayakan kungiyar masu da'awar jihadi sun kai hari kan farar hula a kauyen Kawju.

Rahotanin sun ce an kashe yazidawa akalla tamanin a yankin.

Sai dai lokacin da Amurka ta kadammar da hare hare ta sama a makon daya gabata, shugaba Obama ya ce ya dauki matakin ne domin hana abin da ya kira kisan kare dangi a arewacin Iraki.

Haka kuma gwamnatin ta fuskanci tambayoyi masu zafi akan yadda za ta iya hana kanta shiga cikin rikicin dake kara fadada wanda shugaba Obama ya sha nanata cewa matakin amfani da soja ba zai magance matsalar.