Man U ta hana shigar da kompita filin wasa

Image caption Kulob din ya dauki wannan mataki ne saboda tsaro

Manchester United ta haramtawa magoya bayan kulob din shiga da manya da kananan kompitoci cikin filin wasa

Kulob din ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan wani bayan wani rahoto na leken asiri da ya samu

Manchester United ta kara da cewa matakin ya yi daidai da sabon matakin da aka dauka na binciken kwakwaf akan kayayyakin lataroni a filayen jiragen sama

Kulob din Manchester United ya ce ba kamar a filayen jiragen sama ba, zai yi wahala a caje irin wadannan kayayyakin Lataroni da gaske a filin wasa ta hanyar neman a kunna su

Hakkin mallakar hoto

Wata sanarwar da aka sanya a shafin Kulob din na Intanet tace wannan haramci ya shafi har manya da kananan kompitoci da suka hada da iPad kanana da kuma manyan kayan Lataroni

Wani mai Magana da yawun kulob din ya fadawa BBC cewa kulob din ya dau wannan mataki ne bayan wata shawara da aka bashi, amma bai bayyana inda shawarar ta fito ba.

Ya kara da cewa matakin bashi da alaka ga damuwar da ake nunawa game da magoya bayan da suke amfani da wayoyin tablet wajen nadar bidiyon wasa, garin haka kuma suke kare wasu daga kallon wasan, kamar yadda ake bada rahoto a wasu wurare

Wani mai Magana da yawun Premier League ya ce ‘wannan ba abu bane da muke da alhaki, ko kuma muke da hannu a ciki’

Shi kuwa mai Magana da yawun hukumar kwallon kafa FA bai ce komai ba game da matakin