Sojojin Chadi sun kubutar da wasu 'yan Najeriya

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kungiyar Boko Haram na sace mutane a Najeriya

Rahotanni sun ce Sojojin Kasar Chadi sun kubutar mutane 85 'yan wasu Kauyukan Nijeriya wadanda aka sace mako guda da ya wuce a lokacin wani mummunan hari da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram sun kai a yankunansu.

Wani rahoto ya ce sojojin na Chadi sun tsaida motocin safa-safa da dama dake dauke da mutanen masu bindigogi da mutanen Kauyukan a lokacin binciken da suka saaba yi na kan iyakoki.

Mutanen da aka ceto daga harin da 'yan Boko Haram din suka kai a ranar lahadin da ta wuce, sun shaidawa BBC cewar, 'yan bindigar sun kashe a kalla mutane 28 tare da jikkata wasu da dama kafin su kwashi mutanen da suka yi garkuwar da su a kan kwale-kwale suka tsallaka cikin kasar ta Chadi.

Hukumomin soji a Nijeriya dai ba su da wata sanarwa ta hukuma game da wancan harin, kuma yanzu haka babu wata majiya mai zaman kanta data tabbatar da rahoton kubutar da mutanen.