A Iraki ana ci gaba da gumurzu a kusa da Mosul

Dakarun Kurdawan Iraki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kurdawan Iraki

Wasu majiyoyi na Kurdawan Iraki sun shaidawa BBC cewa dakarun Kurdawa da jiragen saman yakin Amurka ke mara ma baya, na ci gaba da dannawa, a kokarin sake karbe iko da muhimmiyar madatsar ruwan nan da mayakan jihadi na kungiyar ISIS suka kwace.

An ce dakarun Kurdawan sun fara kai farmaki ne da asubahi, kwana guda bayan jiragen yakin Amurka da ma jiragenta marasa matuka sun yi ta luguden bama-bamai.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce hare haren da aka kai sun fada kan motoci sha hudu da mayakan na kungiyar ISIS ke amfani da su, ciki har da wasu na Amurka da mayakan suka kwace daga sojojin Iraki.

A makon jiya ne mayakan suka kwace iko da madatsar ruwan dake kan kogin Tigris, wadda ke samar da wutar lantarki ga arewacin Iraki.