Karancin abinci - dabbobi na mutuwa Mali

Karancin abincin dabbobi a Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karancin abincin dabbobi a Mali

A kasar Mali dake yankin yammacin Afrika, bayan matsalolin tsaro da tashe-tashen hankula da kasar ke fama da su, wasu yankunan ukku na kasar da suka hada da Gao da Kidel da kuma Timbuktu na fuskantar kangin matsalolin kekashewar yanayi sanadiyyar rashin samun ruwan sama da wuri.

A yanzu haka dabobi kimanin dubu dari bakwai ne ke fuskantar barazaranar yunwa saboda rashin abincin da za su ci, a yayinda tuni wasu babobin dubu dari biyu suka mutu sanadiyyar kamuwa da matsanaciyar yunwa.

Dr Saddi Musa wani kwararen Likita a kan tsabtar muhali dake Bamako babban birnin kasar ta Mali, ya baiwa mutane shawarar kada su kuskura su ci naman dabbobin su idan suka mutu.

Karin bayani