Na'ura mai sansana dalolin Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana fasakaurin makudan dalolin Amurka zuwa Mexico

Masu aikata laifi na fasakaurin biliyoyin takardun kudaden Amurka cikin Mexico a kowacce shekara

Amma a yanzu masu gadin kan iyaka zasu sami wani taimako

Ana samar da wata na'ura da zata iya sansana dalolin Amurka kamar yadda karnuka ke sansana warin muggan kwayoyi

A karon farko masu bincike sun gano wani kanshi dake tattare da takardun kudin Amurkar

Dr Joseph Stetter na kamfanin KWJ Engineering ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da aka gano kanshin kudin

Kamfaninsa na kokarin samarwa da 'yan sandan kan iyaka wata na'ura ta binciken kudi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Na'urar da za'a kirkiro zata taimakawa masu gadin kan iyaka

A shekarar data gabata jami'an Amurka sun kwace fiye da dala miliyan 106 da akai fasakaurinsu tsaba zuwa Mexico.

Kuma ana haurawa da irin wadannan kudade kan- iyaka ba tare da an gano su ba, inda ake boyesu cikin kaya da jakankuna da kuma ababan hawa.

A yanzu haka karnuka ne ke gudanar da bincike, amma sai dai horar da su yana daukar lokaci ga kuma tsada.

Domin nemo wata hanya cikin sauri, sashen tsaron cikin gida na Amurkar ya kalubalanci masana kimiyya da su fito da wata na'ura da zata caje kuma zata gano tulin kudaden da mutum yake dauke da su a jaka ko kuma cikin motar sa.

Sai dai wannan na'ura ta sansana kudi itama zata fuskanci kalubale

Daya daga cikin kalubalen kuwa shine dole na'urar tai aiki koda a cikin yanayi ne na kanshin turare da kanshin abinci da hayakin da mota ke fitarwa kamar yadda Dr Suiqiong Li wani mai bincike a kamfanin KWJ ya bayyana