Wasu da ake zaton suna da Ebola sun gudu

Ebola Liberia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'in tsaro na sintiri don kaucewa bore kan Ebola

Ministan yada labarai a Liberia, ya ce har yanzu ana neman mutane 17 a cikin 37 da aka killace saboda zargin suna da cutar Ebola a wata cibiya ta West Point mai yawan jama'a kafin boren da ya janyo sace kayan cibiyar.

Lewis Brown ya ce al'amarin da ya faru a West Point ba shakka babban koma-baya ne tun bayan fara yaki da cutar a Liberiya, ya ce suna aiki don tabbatar da ganin sun gyara wannan matsala.

Ya ce a yanzu suna kokarin bin sawu da bibiyar wadannan mutane domin dawo da su.

Ministan ya ce ragowar ashirin din a yanzu haka suna Cibiyoyin lafiya, a babban asibitin John F. Kennedy, wasu kuma a cibiyar Elwa da ke wajen Monrovia.

Ya ce an rufe cibiyar a yanzu amma dai akwai shirin sake bude ta, ya ce mutanen da ke cibiyar, sun je ne bisa radin kansu.

Karin bayani