Ma'aikatan agaji da ake kashewa sun karu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An fi kashe ma'aikatan agaji a Afghanistan

Adadin ma'aikatan agaji da aka kashe a sassa daban-daban na duniya ya kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba.

A bara, ma'aikatan agajin 155 suka mutu, an kuma jikkata sama da 170 a hare-haren da aka kai musu.

Fiye da rabin hare-haren, sun faru ne a kasar Afghanistan.

Kasashen Syria da Sudan ta Kudu da Pakistan suna daga cikin yankuna masu matukar hadari.

An ba da alkaluman ne a ranar tunawa da ma'aikatan agaji ta duniya don tunawa da ranar da aka kai harin bam a hedkwatar majalisar dinkin duniya dake Bagadaza a shekara ta 2003.