Najeriya za ta binciki boren sojoji

Wasu sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu sojojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike domin tantance gaskiyar boren sojoji a Maiduguri

Kakakin hedikwatar tsaro ta Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade yace basu dauki wannan abu a matsayin bore ba har sai sun kammala bincike sun kuma tabbatar cewa hakan ne.

Olukolade yace bore ba karamin laifi ba ne a aikin soja, kuma bai kamata a yi gaggawar cewa wani mataki da wani soja ya dauka ya kai ga matsayin bore ba, domin kuwa mugun laifi ne, kuma idan ba'a an tabbatar da shi ba, ba za a yi shelar cewa bore ba ne.

Tun da farko a yau wasu sojojin da ke barikin Maimalari a Jihar Borno sun bujirewa umarnin tura su daji domin yaki da 'yan Boko Haram.

Sojojin wadanda yawan su ya haura talatin suka ja tunga da motocinsu a kan hanyar Maiduguri zuwa Bulabiri sun yi korafin cewa basu da isasun makamai da alburusai suna cewa ba za su yarda su yi mutuwar wulakanci domin ko da a ranar Litinin da ta wuce 'yan Boko Haram sun yiwa takwarorinsu kwantar bauna a kan hanya kuma basu da makamai da za su iya maida martani.

Daya daga cikin sojojin da suka yi boren wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa BBC cewa ba za su shiga dajin ba sai an basu isasun kayan aiki da makamai.

Karin bayani