Alqaeda makiya musulunci ne- Al-sheikh

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyoyin Isis da Al-qaeda na ikirarin yin gwagwarmaya don jaddada tsarin musulunci

Malami mafi girma a Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz al-Sheikh, ya ayyana kungiyoyin 'yan gwagwarmaya na Isis da Al-Qaeda a matsayin makiyan addinin musulunci na farko.

A wata sanarwa da ya fitar a binin Riyadh, babban malamin ya ce al'ummar musulmi ne wadanda ayyukan tsaurin ra'ayi na wadannan kungiyoyi ya fi shafa.

Sheikh Abdul Aziz ya ce raba kan al'ummar musulmi babban laifi ne a addinin musulunci.

Wani wakilin BBC ya ce sanarwar ta fito da matsayin Hukumomin Saudiya ne da ke musanta alakar tsarin kasar na bin tsagwaron tafarkin musulunci da akidojin wata kungiya.