Kisan giwaye ya kai intaha a Afrika

Giwayen Afrika na neman karewa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Giwayen Afrika na neman karewa

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa adadin giwayen da ake kashewa ya kai intaha, ana kisan su kowacce shekara fiye da yadda ake haihuwarsu.

Masu binciken sun yi imanin cewa tun a shekara ta 2010 ana kashe kimanin giwaye dubu talatin da biyar kowacce shekara a nahiyar ta Afrika.

Sun yi gargadin cewa idan aka cigaba da kisan na su a haka, za su kare kwata-kwata cikin shekaru dari masu zuwa.

An buga rahoton ne a mujallar masu bincike na Cbiyar binciken Kimiyya ta Kasa.

Jagoran masu binciken George Wittemyer daga Jami'ar jihar Colorado a Amurka ya ce "muna wargaza gandun giwaye, muna yi musu kisan kiyashi a sassa dabam-dabam na nahiyar."

A 'yan shekarun nan, haramtaccen cinikin hauren giwa ya karu matuka, kilo daya na hauren a yanzu ya kai darajar dubban daloli. Karuwar bukatar hauren ne a kasunnin yankin Asia ya kara kururuta kisan giwayen.

A yayinda dama kungiyoyin masu kare muhalli da namun daji suka fada cewar, sakamakon da hakan zai haifar yana da muni, wannan nazarin ya ba da cikakken bayanin tasirin da hakan ke haifarwa ga giwayen Afrika.

Masu binciken sun gano cewar a tsakanin shekara ta 2019 zuwa ta 2013, Afrika ta rasa kimanin kashi bakwai na dukkan giwayen ta a kowacce shekara.

Saboda haihuwar giwayen ta sanya an samu karuwar yawansu da kimanin kashi 5 a kowacce shekara, wannan na nufin, ana kashe dabbobin fiye da yadda ake haihuwar su.

Julian Blank daya daga cikin masu binciken, ya ambata cewar, muddin aka cigaba da kashe giwayen ba kakkautawa, zuwa wani dan lokaci, za su kare.

Karin bayani