Isra'ila ta kai sabon farmaki a Gaza

Hare hare a Gaza Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hare hare a Gaza

Kasar Isra'ila ta kai wasu sababbin hare-hare kan Gaza ta hanyar amfani da jiragen sama, bayan wasu rokokin da aka harba wa Isra'ila daga Gaza, sa'o'i kadan kafin karewar wa'adin wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta baya-bayan nan.

Sojojin Isra'ila sun kai hari kan yankunan Zaitun da Shejaiya da ke gabashin birnin Gaza, da kuma wasu sassan da ke arewaci da kuma kudancin birnin.

Wasu da abin ya faru a kan idonsu sun ce dubban Palasdina na ta tserewa daga gidajensu zuwa sansanonin majalisar dinkin duniya.

Kungiyar Hamas dai ta musunta harba wa Isra'ila rokoki.

Masu aiko wa BBC labarai dai sun ce, da wannan barkewar fadan babu tabbas ko za a ci gaba da tattaunawar sulhun da ake yi da bangarori biyun a Masar ko kuma maganar za ta rushe.

Firayim Ministan Isra'ila, Benyamen Netanyahu dai ya umurci ayarin da ke wakiltar kasarsa da ya fice daga Cairo, yayin da ayarin Palasdinawa a bangare guda ke cewa tattaunawar sulhun ta kakare.