Obama ya yi tir da fille kan Ba'amurke

Image caption Obama ya ce Amurka za ta ci gaba da yin duk abun da ya dace don kare jama'arta

Shugaban Amurka Barak Obama ya bayyana fille kan Ba'amurke dan jarida, James Foley, da kungiyar Isis ta yi a matsayin wata ta'asa da ta dimauta zukatan al'ummar duniya.

Ya ce duniya ta yi watsi da abun da suka yi, ya kara da cewa akidunsu sun gurbata kuma ba su dace da rayuwar karni na 21 ba.

Tun da farko, majalisar tsaro ta kasa a Amurka ta tabbatar da ingancin hoton bidiyon da ke nuna fille kan James Foley.

Hoton bidiyon wanda kungiyar Isis ta sanya a shafin sada zumunta ya fuskanci tofin Allah tsine daga kasashen duniya.

Faransa ta ce kamata ya yi wakilan dindindin na kwamitin tsaro a majalisar dinkin duniya da kuma kasashen larabawa ciki har da Iran su hada karfi wajen yaki da Isis.