Burtaniya ta shiga binciken kashe dan jarida

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahaifiyar James Foley ta bayyana juyayin rashin dan nata da ta ce ya je Syria ne don fito da halin da suke ciki

Jami'an tsaron Burtaniya sun kaddamar da bincike don gano wanda ake zargi da kashe wani Ba'amurke dan jarida, James Foley bayan sace shi a Syria.

An sace dan jaridar ne mai shekaru 40 Shekaru biyu da suka gabata a Syria, daga bisani kuma ya shiga hannun Kungiyar ISIS mai ikirarin kafa daular musulunci.

Firaministan Burtaniya, David Cameroon ya katse hutunsa bayan kungiyar ISIS ta fitar da hoton bidiyo da ke nuna yadda aka fille wa dan jaridar kai.

Hukumomi a Burtaniya na tunanin mai yiwuwa akwai hannun wasu 'yan kasar a kashe wannan dan jarida Ba'amurke, wanda aka ji karin harshen kasar ta Burtaniya a muryar mutumin da ya fille wuyansa.

Yayin da Amurka ita ma ke tantance sahihancin hoton bidiyon, wanda aka wallafa a wani shafin sada zumunta.