An kafa dokar hana fitar dare a Liberia

Hakkin mallakar hoto

An kafa dokar hana fitar dare a Liberia bayan wata hatsaniyar da aka yi dazu, a Manrovia babban birnin kasar.

'Yan sanda sun yi amfani hayaki mai sa kwalla don tarwatsa wasu da suka yi zanga-zanga saboda killace unguwar su da aka yi don hana yaduwar cutar Ebola.

Shaidu sun ce mazauna wurin da suka fusata sun rika jifan jami'an tsaron dake kokarin hana kai komo a yankin da duwatsu, inda aka kai hari kan wata cibiyar kiwon lafiya a karshen makon da ya gabata.

Unguwar dai tana cikin yankin da aka kai hari tare da washe wata cibiyar masu Ebola a karshen mako, lokacin da majinyata 17 da ake zaton suna dauke da cutar Ebola suka bata amma daga bisani aka gano su.

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta ba da umarnin hana zirga-zirgar dare don takaita yaduwar cutar Ebola a fadin kasar.

Yanzu dai adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola ya karu zuwa fiye da 1,200