Yadda macizai ke makalkale bishiya

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Binciken ya nuna abin mamaki ne yadda kowana maciji ke makalkale bishiya fiye da kima don ka da ya fado.

Wani bincike ya gano cewa, wasu nau'in macizai na makalkale bishiya da karfi sosai fiye da kima a lokacin da suke hawan bishiyar.

Binciken ya gano cewa macizan da suke hawa bishiya sukan makalkale ta da karfi sau kashi biyu zuwa biyar fiye da yadda ya kamata su rike ta ba tare da wani hadari na fadowa ba.

A karon farko masana kimiyya sun yi amfani da wani bututu domin gano yadda maciji ke hawa bishiya ko tafiya a kanta.

Masanan sun gano cewa maciji ya fi damuwa da kare lafiyarsa, don ka da ya fado, fiye da komai a lokacin da yake bin bishiya.

Hakkin mallakar hoto bruce jayne
Image caption Maciji ya makalkale reshen bishiya

Wanda hakan ya sa yake rike bishiyar fiye da yadda ya wajaba ba don komai ba sai domin ka da ya fado.

Dr Greg Byrnes, ne ya jagoranci binciken a jami'ar Cincinnati tare da Farfesa Bruce Jayne, kuma aka wallafa a mujallar Biology Letters.

Binciken ne na farko da ke nuna, yadda macizai ke mayar da hankali sosai kan lafiyarsu, yayin hawa bishiya, ko tafiya a kan bishiya.

Dr Byrnes ya ce, ''kamar kai ne za ka tsallaka wata korama, za ka auna irin tsallen da za ka yi, daga nesa ne ko daga kusa ?''