Boko Haram ta karbe kwalejin 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akwai kalubale kan sabon Sufeto Janar, Sulaiman Abba

Rahotanni daga garin Gwoza a jihar Borno a Najeriya na cewa kungiyar Boko Haram ta karbe iko da wata makarantar horar da 'yan sanda da ke Limankara.

Mazauna yankin sun ce maharan da suka karbe makarantar sun fito ne daga garin Gwoza wanda suka karbe iko da shi makonni biyu da suka wuce.

Haka zalika mazauna garin Buni Yadi da ke kusa da Yobe sun ce garin ya koma karkashin kungiyar ta Boko Haram.

Kawo yanzu dai jami'an tsaron kasar ba su kai ga cewa komai ba game da rahotannin karbe makarantar 'yan sandan da kuma garin na Buni Yadi.

A cikin 'yan watannin nan kungiyar Boko Haram na ta karbe iko da garuruwa a jihohin Borno da Yobe.