Sakonnin ISIS sun gagara

Shafin sada zumunta na diaspora da mayakan kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ke amfani da shi wajen aikewa da sakonni ya ce ba zai iya hana kungiyar yin amfani da shafin ba wajen yada bayanan aikace-aikacen su.

Manhajar Diaspora ta kasance wata kafa ta tattaro bayanai daga wasu runbunan tattara bayanai ta intanet masu yawa, kuma tafi karfin kulawar mutun daya.

Mayakan kungiyar sun koma yin amfani da manhajar Diaspora wajen yada aikace-aikacen su saboda kokarin rufe hanyoyin sadarwar kungiyar ta manhajar Twitter da ake.

Hakkin mallakar hoto bbc

Mamallakan manhajar ta Diaspora su ka ce sun damu matuka da aikace-aikacen kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci.

A wani rahoto da suka buga ta shafin su na intanet, Mamallakan manhajar Diasporan suka ce jaridu da yawa sun bada labarin cewa manbobin kungiyar sun bude hanyoyi sadarwa ta manhajar don yayata aikace-aikacen su.

''A can baya, suna amfani da Twitter da sauran manhajoji, amma yanzu suna kaura daga gare su zuwa wasu hanyoyin na kyauta masu sassaucin sha'ani''.

Diaspora ya ce suna kokarin tuntubar masu kula runbunan tattatar bayanai da nufin ankarar da su a ga me da matsalar bayanan aikace-aikace masu kishin addini, da kuma hadarin adana ire-iren bayanan.

Hakkin mallakar hoto AFP

Kafin ta mai da hankali ga shafin Diaspora, kungiyar ISIS ta na aika sakonnin ta ne Twitter.

Sai dai a 'yan makonnin da suka gabata, shafin Twitter ya matsa wajen rufe damar sadarwa da mambobin kungiyar da masu goyan bayan su ke da ita a Twitter.

Shafin na Twitter ya kuma fadada rufe hanyoyin sadarwan, inda ya hada da duk wani mai amfani da shafin da ya sanya hotunan bidiyon kisan da mayakan kungiyar ISIS sukayi wa Ba'amurken dan jaridan nan, James Foley.

Amma shafin Diaspora, saboda irin yadda ya ke, ba zai iya daukan matakin da shafin Twitter ya dauka ba

Jamie Bartlett, mawallafin wani littafi akan shafukan sadarwa na intanet, 'the Dark Net' ya ce ba abin mamaki ba ne yadda kungiyar ta ISIS ta ko ma wa shafin Diaspora don cigana da yada sakonnin ta.