Ebola: Kasuwar naman Biri ta yi kasa a Nigeria

Image caption Cutar Ebola ta bulla a Najeriya a watan Yuli bayan dan Liberiya mai dauke da cutar ya je Najeriyar

A Najeriya mutane na kauracewa wuraren da ake sayar da naman Biri da barewa da jemage da dangoginsu sakamakon bullar cutar Ebola a kasar.

Hakan ya sa kasuwar irin wadannan nama ta yi kasa sosai a sassa daban-dabn na kasar.

A baya dai mutane da dama ne ke zuwa irin wadannan wurare, bayan sun tashi daga aiki ko kuma a ranakun Asabar da Lahadi domin cin naman irin wadannan dabbobi da kuma shan barasa.

Kawo yanzu dai mutane biyar ne hukumomi suka tabbatar sun mutu sakamakon cutar Ebola a Najeriya, yayin da ake ci gaba da yunkurin hana bazuwar cutar.