Ebola:An hana 'yan Liberia shiga kasashe

Image caption Ita ma Liberia ta dauki matakin hana zirga-zirga tsakanin 'yan kasarta don hana bazuwar cutar

Afrika ta Kudu da Senegal sun hana matafiya daga kasar Liberia, daya daga cikin kasashen da annobar Ebola ta fi kamari, shiga kasashen.

Hukumomin kasashen biyu sun dauki matakin ne duk da shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar ta hana yin hakan.

Sama da mutane 1,300 ne cutar Ebolan ta hallaka,a Afrika ta yamma kawo yanzu, galibinsu a Liberia da Guinea da kuma Saliyo.

A halin da ake ciki kuma wani asibiti a Amurka ya sallami wasu, masu aikin yada bushara ko wa'azin kirista, biyu, da ake yi wa maganin cutar, bayan da suka warke.

An yi amfani da maganin gwaji ne a kan mutanen, wanda a baya ba a taba amfani da shi a kan mutane ba, amma likitoci sun ce ba su sani ba ko hakan ne ya taimaka suka samu lafiya.