Google ya cire hanyoyin samun labarai na BBC

Kamfanin Google ya cire hanyoyin samun labarai na BBC guda 12 tun bayan da tarayyar turai ta zartar da wasu dokoki da ake cece ku ce akansu a watan mayun daya gabata.

Labaran sun hada da shariar da aka yi wasu inda ake zarginsu da hada bam a yankin Ireland shekaru 13 da suka gabata da kuma takaddama akan wani kare da ya bata.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamfanin Google ya sanar da BBC da hanyoyin samun labarai da ya cire , sai dai be bayana ko su wanene suka nemi a cire labaran ba.

A baya bayanan Google ya bayana cewa yana samun bukatu daga wurin mutane akan ya cire wasu shafuka internet tun bayan da kotun turai ta yanke hukunci a watani uku da suka gabata.

A watan daya gabata ne kamfanin ya shaidawa hukumar dake sa ido cewa ya samu bayanai dubu 91 akan ya cire shafuka dubu 328 .

Ya kuma ce ya cire kashi 50 cikin dari daga ciki.

A cikin hanyoyin samun labarai na BBC 12 da Google ya cire , hudu sun hada da sashin sharhi akan al'amuran yau da kullum na tsohon editan BBC akan kasuwanci Robert Peston wanda aka cire a watan yulin daya gabata.

Sauran sun hada da batutuwan kotu, ciki har da shariar da aka yi wa wasu mutane uku da ake tuhuma da mallakar naurar hada bam a yankin Ireland.

Akwai labaran da suka shafi shariar da aka yi wa wata mata da aka samu da laifin tafiyar da gidan mata masu zaman kansu a shekarar 2003.

Sauran labaran da aka cire sun hada da takaddamar tsakanin wasu iyalai akan wani kare a shekarar 2002.