Jirgin sama mai fata irin ta mutum

Image caption Amfani da wannan fasaha a jirgin ko mota zai iya kare aukuwar hadarinsu a wasu lokutan.

Ana shirin kera jirgin sama wanda za a lillibe jikinsa da na'urori masu aiki kamar yadda fatar jikin mutum ke yi.

Aikin na'urorin wadanda za su kasance 'yan mitsi-mitsi kamar girman kwayar zarra shi ne, za su iya tantance lokacin da wani abu zai iya samun jirgin na illa ko zafi ko sanyi da sauransu.

Kamar yadda dan adam ke yi idan ya fara jin alamun wani yanayi a jikinsa ta hanyar fatarsa, zai dauki mataki, haka wannan fasaha za ta sa a dauki matakin kare jirgin daga yanayin da ke fuskantarsa.

Haka kuma na'urorin za su iya auna gudu da tafiya da yanayin matsuwa da zafi da kuma sanyi da jirgin ke ciki.

Image caption Siffar irin jiragen saman da za a iya kerawa nan gaba

Babbar jami'ar bincike a hukumar BAE ta Birtaniya, Lydia Hyde, ta ce ta yi tunanin kirkirar wannan fasaha ne yayin nazarin na'urar busar da kayan wankinta.

Nau'rar busar da kayan wankin dai tana aiki ne ta yadda wata fasaha a jikinta ke hana ta yin zafin da ya wuce kima da zai iya kona ko lalata tufafi.

Mai binciken, ta ce, 'nazarin wannan na'ura ne ya sa na ga za a iya kirkirar 'yan mitsi-mitsin na'urori masu ayyuka da dama, da za su maye manya-manya masu tsada.

Ta kara da cewa, wannan ne kuma ya ba ta tunanin kirkirar jirgin sama ko mota ko jiragen ruwa, da za a iya lullube su da wadannan mitsi-mitsin na'urori da za su iya nazarin yanayin muhallin da jirgin ko motar ta ke.

Za a iya sanya 'yan kananan na'urorin a jikin jirgin ko motar a fentinsu.

Za kuma a iya daukar matakin gyara jirgin ko motar a kan lokaci idan aka fahimci matsalar da ta same shi, ta hanyar wadannan 'yan na'urori.

Baya ga haka za kuma a iya amfani da wannan fasaha, a bututun ruwan.

Idan lokacin tsananin sanyi ne, 'yar naurar da ke jiki za ta kunna wata na'urar mai sanya zafi da za ta hana fashewar bututun.