Israila za ta cigaba da amfani da karfin soja

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Benjamin Netanyahu

Firai ministan Israila, Benjamin Netanyahu , ya ce za a cigaba da amfani da matakin soja a zirin Gaza har sai an samu tabacin tsaro a kasar.

Mayakan kungiyar Hamas sun harba rokoki masu yawa cikin Isra'ila tun bayan wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki goma.

Isra'ila ta mai da martani da lugudan wuta kimanin dari ta sama akan Gaza.

Kungiyar Hamas ta ce shugaban mayakan ta, Mohammed Deif ya tsallake wani hari akan rayuwar sa da sojojin Isra'ila suka kai ta sama ranar Talata, amma matar sa da jaririn ta sun mutu a harin.

Dubban 'yan zaman makoki ne suka fito a unguwanni a Gaza domin jana'izar matar da jaririn nata, tare da ambaton daukar fansa