Thailand: Prayuth ya zama Firaminista

Hakkin mallakar hoto
Image caption Janar Prayuth Chan-Ocha

An nada Janar din kasar Thailand dinnan da ya kwace iko a wani juyin mulkin soji a farkon shekaran nan, Prayuth Chan-Ocha, a matsayin Firaminsta.

Shi kadai ne dan takarar da ya tsaya zabe a majalisar dokokin kasar ta Thailand da soji suka kafa.

Janar din ya yi alkawarin kawo sauye-sauye na siyasa masu tsauri domin hana sake aukuwar rikice-rikicen da kasar ta yi fama da su a 'yan shekarun nan.

Sai dai kuma wakilin BBC a Bangkok ya ce, masu sukan lamirin janar din na ganin aniyarsa kawai ita ce watsa jamiyyar tsohuwar Firaministan kasar, Thaksin Shinawatra.