Kwamitin sulhu ya gaza: inji Pillay

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto un news center
Image caption Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Babbar jami'ar hukumar kare hakkin bil'adama, Navi Pillay ta yi kakkausan suka ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya saboda abinda ta kira gazawar shi wajen magance rikice rikice.

A wani jawabi da ta gabatar kwanaki kadan da suka rage tayi murabus daga mukaminta, Madam Navi ta ce kwamitin sulhun ya ki ya tashi tsaye wa rikice-rikice da ake fama da su a kasashen duniya, tare da kawo karshen su.

Ta ce inda kwamitin ya jajirce, da an iya tseratar da dubban daruruwan rayukan mutane daga halaka.

Madam Navi ta yi nuni da rikice-rikicen da ake fama dasu a Afghanistan, da Iraki da Ukraine da kuma kasar Jamhoriyar Afrika ta Tsakiya a matsayin musalan gazawar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.