Amurka: yunkurin dakatar da tarzoma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babban jami'in 'yan sandan Ferguson na ganin tarzomar ta dauko lafawa

Babban lauyan gwamnatin Amurka, wato attorney janar, Eric Holder na ganawa da 'yan sanda da mazauna garin Ferguson na St Louis, saboda tarzomar da ake ta yi, tun sati biyun da suka gabata, kan kisan da 'yan sanda suka yi wa, wani matashi bakar fata, da ba ya dauke da wani makami.

Mr Holder, ya ce, yana fatan alkawarin da ya yi na gudanar da cikakken bincike kan kisan, Micheal Brown, ya kwantar da hankali.

Attorney janar din, ya kuma gana da iyayen, matashin, yayin da kuma wani ayarin masu taimaka wa alkali yanke hukunci ke shirin, fara sauraren shedu kan kisan.