'Kungiyar ISIS babbar barazana ce'

Chuck Hagel Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel

Amurka ta ce kungiyar da ke kiran kanta Daular musulunci, ita ce barazana mafi hadari da ta taba fuskanta a lokacin nan, kuma ta ce wajibi ne ta murkushe ta a Iraqi da Syria.

Amurkan ta ce hare haren da take kai wa mayakan kungiyar ta sama sun taimaka wajen rage karsashinta, amma kuma akwai bukatar samar da wata runduna ta soji ta hadaka domin gamawa da kungiyar baki daya.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, ya bayyana kungiyar a matsayin, wadda take da kwarewa da kuma samun kudade sosai, fiye da duk wata da Amurka ta gani a baya.

Ya ce, '' ba wai kungiyar 'yan tadda ba ce kawai, ta wuce haka, suna da kwarewa ta dabaru da kuma ta karfin soji, ana kuma basu kudaden tafiyar da ayyukansu sosai.

Amurkan ta kuma fara gudanar da binciken kisan dan jaridar nan dan kasarta, James Foley, da 'yan kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci suka yi.