Ebola ta shafi harkokin tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto AP

Duk da mace-macen mutane fiye da 1,300 sakamakon cutar Ebola a Afirka ta Yamma, kwayoyin cutar ba kawai ci gaba da barazana ga tsarin lafiya cikin gaggawa suke yi ba, har kuma suna yin nakasu ga tattalin arzikin kasashen

Guinea, Liberia da kuma Saliyo.

Ministan Noma a Saliyo, Joseph Sam Sesay ya fada wa BBC cewa tattalin arzikin kasar ya ragu da kaso 30 cikin 100, ya ce shugaba Ernest Bai Koroma ne ya bayyana a wani taro na musammam da Ministocinsa labarin mai sanyaya zuciya.

Mr. Sesay ya kara da cewa bangaren noma ne cutar Ebolar ta fi shafa, don kuwa mafi yawan al'ummar Saliyo Manoma ne.

A yanzu cutar ta addabi sha biyu cikin 13 na lardunan Saliyo, ko da yake cutar ta fi muni a yankin gabashi, kusa da kan iyakarta da Laberiya da kuma Guinea.

'Yan sanda da dakarun soji sun sanya shingaye a kan tituna don hana zirga-zirgar manoma da ma'aikatan kwadago, gami da safarar kayayyaki da nufin hana mutane guduwa daga inda cutar ta fi shafa zuwa wasu yankuna.

Karancin abinci

Babban jami'in shirin raya kasashe na Majalisar Dinkin Duniya, David McLachlan-Karr, na ganin cewa kafa shingayen na da matukar muhimmanci wajen shawo kan cutar, ko da yake ya yarda cewa an kassara harkokin noma a Saliyo.

Tasirin cutar kan tattalin arzikin Guinea da Laberiya, ka iya zama mara muni sosai, sai dai har yanzu akwai fargaba.

Babban Bankin duniya ya ce ana sa ran faduwar alkaluman ababen da kasar Guinea ke samarwa a cikin gida daga kaso 4.5 zuwa kaso 3.5 cikin 100.

Hakkin mallakar hoto Getty

Tasirin Ebola a kan ma'adanai

Babban kamfanin mulmula karfe a Duniya ArcelorMittal ya fuskanci cikas a yunkurinsa na fadada wata mahakar tamarsa a Laberiya, bayan 'yan kwangilar da ke aikin sun fice daga kasar.

Haka zalika, kamfanin hakar kuza na Vale ya kwashe wasu manyan ma'aikatansa shida daga dajin Simandou da ke gabashin Guinea, ya kuma bai wa saura hutu.

Shi ma kamfanin London Mining ya kwashe wasu ma'aikata da aikinsu bai zama dole ba daga Saliyo, wadda ta dogaro kacokam kan ma'adanai don bunkasar tattalin arzikinta.

Rufe kan iyakoki

A Saliyo, Bankuna sun rage lokacin budewa da sa'a biyu don rage ta'ammali da abokan hulda, yayin da mutane musamman baki masu yawon shakatawa suka gujewa gidajen otel.

Rufe kan iyakoki a Afirka ta yamma da dakatar da jigilar jiragen sama ya yi nakasu ga harkokin kasuwanci, lamarin da ya takaita fiton kayayyaki tsakanin wasu kasashe.

Batu na baya-bayan nan shi ne doguwar iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru ta rufe, sai kuma dakatar da sufuri da kamfanin jiragen sama na Kenya Airways ya yi zuwa kasashen Saliyo da Laberiya.

Hakkin mallakar hoto Getty

Da ma duk kasashen uku na Afrika ta Yamma matalauta ne, sai dai barazanar Ebola ka iya kara talauta su, Laberiya da Saliyo sun fara murmurewa daga munanan yake-yaken basasa, inda suke kokarin sake gina tattalin arzikinsu.

A lokaci guda kuma, masu zuba jari na duniya cikin kosawa sun zuba ido don ganin karshen wannan lamari, babbar jami'ar kamfanin ayyukan tuntuba a Africa@Work da ke birnin Johannesburgh, Dianna Games, ta ce fargaba game da cutar ka iya bata yunkurin farfado da tattalin arzikin Afrika a baya-bayan nan.