Ebola: 'za ta dauki watanni a kasashe'

Hakkin mallakar hoto c
Image caption Kawo yanzu cutar ta hallaka mutane sama da 1,400, a Liberia da Guinea da Saliyo da kuma Najeriya.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce yadda cutar Ebola ke bazuwa a Yammacin Afrika, abu ne da ba a taba gani ba, kuma za a dauki watanni na aiki tukuru kafin a shawokan annobar.

Hukumar ta kuma kara da gargadin cewa, ana takaita girman bannar da cutar ke yi, saboda dalilai da dama, kamar, yadda, wasu iyalai ke boye 'yan uwansu da suka kamu da cutar a gidajensu.

Ministan watsa labarai na Liberia daya daga cikin kasashen da cutar ta addaba a Yammacin Afrika, Lewis Brown, ya ce, yaki da cutar har yanzu ya dogara ne a kan daukar matakan hana bazuwarta.

kuma ya gargadi mutane da su ka da su saki jiki cewa ana kan hanyar samun maganinta.

Ya ce, '' ba ma son mutane su yi watsi da matakan rigakafi daga cutar, da zummar cewa, yanzu muna da maganinta, har yanzu ba mu da cikakken sani a kanta.''

Karin bayani