Hadarin mota a Masar ya kashe mutane 33

Image caption Wani daga cikin irin haduran motocin safa da ake samu a Masar

Wasu motocin safa biyu sun yi karo a yankin Sinai na kasar Masar, inda mutane akalla 33 suka mutu.

Hadarin ya auku ne a tazarar kilomita kusan 50 daga wurin shakatawa na Sharm El-Sheik.

Karon ya kai ga har daya daga cikin motocin ta kife.

Motocin daukar marassa lafiya 30 aka tura domin jigilar wadanda suka samu raunuka zuwa asibiticocin da ke kusa.

Masar na daya daga cikin kasashen da a duniya aka fi samun haduran ababan hawa, saboda tukin ganganci ko rashin kula da lafiyar ababan hawa da kuma rashin kyawun tituna.