An kashe mutane 18 a Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan sa-kai a Gaza

Rahotanni daga Gaza sun ce an kashe wasu mutane 18 da ake zargin masu kai wa Isra'ila kwarmato ne.

Shafukan labarai na intanet da ke da kusanci da kungiyar Hamas sun ce 11 daga cikin wadanda ake zargin an kashe su ne ta hanyar bindigewa a wani ofishin 'yan sanda.

Wani shaida da kuma wata majiyar labarai a Gaza ta ce wasu 'yan bindigar da suka rufe fuskokinsu ne suka kashe karin masu leken asiri bakwai a kusa da wani masallaci.

Kisan ya zo ne kwana daya bayan wani harin da Isra'ila ta kai ta sama da ya kashe kwamandojin sojin Hamas uku.

Karin bayani