Netanyahu: Hamas za ta dandana kudarta

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Netanyahu ya umarci sojojin Isra'ila su tsananta hare-hare a Gaza

Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu , ya ce Hamas, za ta dandana kudarta a kan mutuwar wani yaro dan shekara hudu da wani makamin roka da ta harba daga Gaza ya kashe a yankin Isra'ilan.

Yaron dai shi ne farar hula na hudu, kuma yaro na farko a bangaren Isra'ila da ya mutu a rikicin.

Mr Netanyahu , ya umarci sojojin Isra'ilan da su tsananta hare haren da suke kaiwa kan mayakan Falasdinawa.

A hare haren Isra'ilan na cikin dare, ma'aikatan lafiya da wasu ganau sun ce, ta kashe mutane uku a wani gida a tsakiyar Gaza.

Sama da Falasdinawa 2000 ne da suka hada da kananan yara fiye da 400 suka mutu a hare haren na Isra'ilan a Gaza, tun lokacin da fadan ya fara a farkon watan Yuli.