Nijar za ta sayo jirgin sama mai tsada

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gwamnati ta ce, ba Shugaban kasar ne kadai zai yi amfani da jirgin ba

Gwamnatin Nijar ta ware kimanin CFA bilyan 22 dan sayen jirgin sama ga shugaban kasar,abin da ya jawo cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar.

Gwamnatin na shirin hakan ne yayin da hukumar kididdiga ta majalisar dinkin duniya ta sanya kasar a matsayin ta karshe a duniya a cigaban al'umma.

Jam'iyyun adawa da wasu kungiyoyin fararen hula a kasar sun ce shirin siyo jirgin bai dace ba a yanzu.

Inda suka ce kamata yayi a kashe kudin a ayyukan da zasu amfani jama'a.

Wani jami'in gwamnati Nijar din ya ce babu wani talauci da siyo jirgin zai haifar a kasar.

Kuma ya ce ba shugaban kasa ba ne kadai zai yi amfani da jirgin domin mallakar kasar ce baki daya.

Ya ce in an siyo jirgin, za a yi amfani da shi a sauran aikace-aikace a kasar masu muhimmanci.