Ebola ta kama karin mutane biyu a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ministan kiwon Lafiya a Nigeria, Dr Onyebuchi Chukwu

Ministan Lafiya a Nigeria, Dr Onyebuchi Chukwu ya sanar da cewa an samu karin mutane biyu da ke dauke da kwayar cutar Ebola a kasar.

A cewarsa, mutane biyun da suka kamu da cutar, iyalan wadanda suka kamu da cutar ce sakamakon kusantar dan Liberia, Patrick Sawyer wanda ya shigo da cutar Ebolar Nigeria.

Ministan ya ce wadannan mutane biyu su ne na farko wadanda suka kamu da cutar sakamakon mu'amala da mutanen da suka kamu da cutar kai tsaye ta hanyar dan kasar ta Liberia.

Kawo yanzu dai cutar ta Ebola ta kashe mutane biyar a Nigeria.

Nigeria dai na daukar matakan hana yaduwar cutar Ebola, musamman ta hanyar killace mutanen da ake tunanin suna dauke da kwayar cutar.

Sama da mutane 1,300 ne cutar Ebola ta hallaka a Afrika ta yamma kawo yanzu, galibinsu a Liberia da Guinea da kuma Saliyo.