Taron samar da tsaro kan iyakokin Najeriya

Iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru

Hukumomin shiga da fuce a Najeriya sun shirya wani taron domin lalubo hanyoyin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta daga kungiyar Boko Haram .

Daga cikin abubuwan da taron zai duba sun hada da rashin isassun kudade da kuma rashin sabunta dokar da hukumar ke gudanar da ayyukanta wajen kare iyakokin kasar.

Mahalata taron sun bayana cewa rashin isasun ma'aikata na kawo cikas ga aikin tabbatar da tsaro a iyakokin kasar.

Idan an jima a yau ne ake sa ran kammala taron inda mahalata zasu bayar da shawarwari ga mahukuntan kasar .

Ana sa ran shawarwarin zasu taimka wajen shawo kan kalubalen tsaro da ake fuskanta daga kungiyar Boko Haram game da kai hare hare cikin kasar daga kasashe makwabta