Sabuwar kwamfuta Nook Tablet

Shahararren kamfanin dillancin littattafan karatu da kayan nazari a Amurka, Barnes & Noble ya gabatar da wata sabuwar karamar kwamfutar karatu ta Nook Tablet a kasuwa, wadda ke da zubin Samsung Tablet.

Ita ce za ta maye gurbin kwamfutar Nook HD+ da kamfanin ya kera daga farko.

Kamfanin Barnes & Noble ya na tallata kwamfutar wadda itace irin ta ta farko da aka kera akan manhajar Android domin karatu kawai, saboda wasu manhajojin Nook da ta zo da su daga kamfani.

Sai dai kyawun yadda Nook Tablet ke fidda rubutu bai kai na makamanciyarta Kobo Arc 7HD ba, wadda itama ke sarrafuwa da Android.

Hakkin mallakar hoto SAMSUNG

Wani masanin kwamfutocin tablet, Ben Wood, ya ce sai anyi da gaske wajen ganin kwamfutar Nook Tablet ta yi kasuwa.

''Ana cigaba da samun rashin sha'awar amfani da kwamfutocin Tablet masu saukin kudi daga wuraren jama'a'' inji Wood na kamfanin CCS Insight.

''Koda yake Nook Tablet ta zo da zubi na daban, farashin ta zai kasance a layi daya da na sauran kwamfutocin Tablet da zasu bayyana a kasuwa zuwa lokacin Krismeti''.

''Kwamfutocin tablet na karatu na kamfanin Amazon sun kakkame kasuwa, amma abu daya da yasa na jinjina ma kamfanin Barnes & Noble shi ne hada hannu da su kayi da kamfanin Samsung, domin hakan zai sa kwamfutar Nook Tablet ta yi inganci''.

Kwamfutocin Samsung Tablet masu fadin inci 7 sun sha gaban na Amazon, domin su suna da damar shiga kasuwar manhajoji ta Google Play, yayinda kwamfutocin Amazon Tablets runbun manhajoji marasa yawa su ke da damar shiga.

Hakkin mallakar hoto n

Farashin sabuwar kwamfutar Nook Tablet dala 179, ya fi sauki akan farashin kwamfutar karatu ta Kindle Fire HDX, da kuma ta Kobo Arc 7HD.

Sai dai bakake a kwamfutar Nook Tablet ba su kai na Kindle Fire HDX, da kuma ta Kobo Arc 7HD fita tangaran ba.

Mujallu da hotunan bidiyo a Nook Tablet ba sa kunsan komai da komai kamar yadda su ke a Kindle Fire HDX, da kuma ta Kobo Arc 7HD.

A halin yanzu, a kasuwannin Amurka ne kadai ake samun kwamfutar Nook Tablet mai zubin Samsung Galaxy Tab 4.