An kashe mutane 190,000 a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin Syria ya raba dubban mutane da muhallansu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da dubu 190 ne aka kashe a Syria tun lokacin da aka soma rikici a kasar shekaru uku da suka wuce.

Wannan adadin ya rubanya idan aka kwatanta da watanni 12 da suka wuce.

Ofishin hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya wanda ya fitar da alkaluman, ya ce an gano adadin ne sakamakon gano sunaye da bayanai kan mamatan, kuma adadin zai iya zarta haka.

Galibin wadanda aka kashe maza ne sannan yara 'yan kasa da shekaru 10 fiye da 2,000 suma sun gamu da ajalinsu.

Babbar jami'ar hukumar kare hakkin bil'adama, ta majalisar dinkin duniya Navi Pillay, ta yi kakkausar suka ga kwamitin sulhu na Majalisar saboda abin da ta kira gazawar shi wajen magance rikice-rikice.

A jawabinta kwanaki kadan kafin ta sauka daga kujerar ta, Ms Pillay, ta ce kwamitin sulhun ya gaza daukar mataki kan magance tarin rikice-rikice a duniya, kuma sau da dama, ba shi da karfin hali ko aniyar magance tashin hankali.