CAR: An nada Majalisar Ministoci

Firaministan CAR Mahamat Kamoun Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firaministan CAR Mahamat Kamoun

Firaministan Jamhuriyar tsakiyar Afirka Mahamat Kamoun ya nada majalisar ministoci mai mambobi talatin da daya.

Wadanda aka nada din sun hada da wakilan kungiyoyi biyu da suka shiga mummunan gaba da juna da kuma tashe tashen hankula fiye da shekara daya da ta wuce.

Kasar ta Jamhuriyar tsakiyar Afirka ta rabu gida biyu tsakanin 'yan tawayen Seleka wadanda galibinsu musulmi ne da kuma 'yan tawayen anti-Balaka ta kiristoci.

An zargi bangarorin biyu da keta haddin bil Adama.

Tun da farko shugabar gwamnatin wucin gadi Catherine Samba-Panza ta nanata amanna da cancantar Mr Kamoun na jagorantar kasar ya zuwa zaben da za'a gudanar a badi.

Karin bayani