Likitoci sun janye yajin aiki a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani likita a bakin aiki a Potiskum ta jihar Yobe

Kungiyar likitocin Najeriya ta yanke shawarar janye yajin aikin sama da makwanni shida da ta ke yi daga ranar Lahadin nan.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne a karshen taron da ta yi ranar Asabar a Abuja, sakamakon shiga tsakani da ta ce wasu manyan jami'an gwamnati sun yi .

Sai dai ma'ajin kungiyar likitocin Dokta Abubakar Abdurramham ya sheda wa BBC cewa gwamnati ba ta biya musu bukatun da suka kai su ga yajin aikin ba gaba daya.

Amma dai sakamakon shiga tsakani da wasu manyan jami'an gwamnati irinsu Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriyar David Mark suka yi, da musu alkawarin ganin an biya musu bukatun suka janye.

Kungiyar ta kuma ce ganin yadda jama'a suke wahala da kuma bullar annobar Ebola ya kamata su janye yajin aikin.

Wakilan gwamnatin sun kuma tabbatar wa likitocin za a mayar da likitocin nan masu neman kwarewa 16,000 da gwamnati ta kora daga aiki, bakin aikinsu, ba tare da wani sharadi ba, da zarar kungiyr ta dawo aiki.

Amma kuma kungiyar ta ce idan gwamnati ta kasa biya wa likitocin bukatun da suka kai su ga yajin aikin zuwa lokacin da za su yi taro a birnin Awka na Anambra, nan gaba za su sake komawa yajin aikin.