Abbas ya bukaci tsagaita wuta a Gaza

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya bukaci komawa tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ba tare da jinkiri ba domin kare karuwar hasarar rayuka.

Abbas ya yi kiran ne a birnin Alkahira bayan ganawa da shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi.

Jami'an Masar ne dai ke shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wutar tsakanin Israila da Falasdinawa.

Jami'an lafiya sun ce wani hari ta sama da Israila ta kai Gaza a ranar Asabar din nan ya hallakja wasu mutane biyar dangin iyali daya.

Shugaban Falasdinawan Mahmoud Abbas ya ce dole ne a yi hanzarin tsagaita wutar.

" Yace me ya sa za a rika kai sabbin hare hare akan Gaza ko sauran wurare kamar gabar yamma duk bayan shekaru biyu? Dole ne a samo masalaha ta dundundun."

Karin bayani