Jonathan: Falconets ku lallasa Jamus

Hakkin mallakar hoto NFF
Image caption Shugaba Jonathan ya tabbatar wa 'yan wasan Falconets Najeriya zata yi alfahari da su idan suka ciyo kofi

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya tattauna da 'yan kungiyar kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekaru 20 na kasar, a wani yunkuri na karfafa musu gwiwa a karawar da zasu yi yau Lahadi da kasar Jamus a wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Canada.

Cikin wata sanarwa, mai taimakawa Shugaban kan sha'anin yada labarai, Reuben Abati ya ce Shugaba Jonathan din wanda ke kan wata ziyara a Jamus, yayi fatan 'yan kungiyar ta Falconets za su yi wa kasar su abin alfahari.

Shugaban ya yi magana da 'yan wasan ne ta waya a sansanin su dake Montreal a Canada, inda ya yaba da kokarin da sukayi na kai wa ga zagayen karshe a gasar.

Ya bukaci su da su zage damtse don ganin sun lallasa takwarorin su na Jamus, don su zarce kokarin da sukayi a gasar ta shekarar 2010 inda suka zo na biyu.

Hakan ya ce zai kawo annashuwa da abin alfahari ga 'yan Najeriya, musanman masu sha'awar kwallon kafa.

Shugaba Jonathan ya ce yana fatan tarbar 'yan wasan a Abuja a matsayin zakaru, inda ya basu tabbacin cewa gwamnati da sauran 'yan Najeriya za su zamo masu alfahari da su in suka yi nasara.