'Yan tawaye: A maido tsohuwar majalisa

Filin jirgin sama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Filin jirgin sama

Sabuwar Majalisar dokokin Libya ta yi Allah wadai da karbe iko da babban filin jirgin sama na Tripoli da wata hadakar kawance ta wasu kungiyoyin 'yan tawaye, wadanda majalisar ta bayyana a matsayin 'yan ta'adda ta yi.

Majalisar ta ce yanzu, ya halatta sojojin Libya su yaki hadakar kawancen ta 'yan tawayen.

Hadakar ta kunshi 'yan gwagwarmaya masu kishin Islama, da kuma mayaka daga garin Misrata.

Wani mai magana da yawun hadakar kawancen ya ce sabuwar majalisar dokokin Libyan haramtacciya ce, sannan yayi kiran a dawo da tsohuwar majalisar shugabancin kasar wadda masu kishin Islama suka fi rinjaye a cikinta.