Neman jirgin Malaysia zai yi tsanani

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ya zuwa yanzu jirgin Holland ya bincike yankin da ya kai zurfin kusan mita 6, 000.

Zagaye na gaba na neman jirgin saman Malaysian nan mai lamba MH370 da ya yi batan dabo zai shiga mataki mai tsananin wuya.

Bayanan da aka tattara akan yanayin karkashin teku a yammacin Australia, ya tabbatar kasan tekun a wasu wuraren yana da kwazazzabai sosai.

A yanzu jiragen ruwa biyu, Fugro Equator da Zhu Kezhen, suna aikin laluben tarkacen jirgin a yanki mai murabba'in kilo mita 60,000 a teku.

Binciken na yanzu za a yi shi ne daki-daki inda za a yi amfani da manyan na'urorin da za a rika jan su a ruwan da kuma wadanda za a sanya a karkashin teku.

Ana sa ran fara wannan kashi na aikin ne a kusan karshen watan Satumba, wanda kuma hukumomin Australia suka yi gargadin cewa zai iya kai wa shekara daya kafin a kammala shi.

Hakkin mallakar hoto AP

A yanzu jirgin ruwan kasar Holland, Fugro Equator da na China Zhu Kezhen suna hada taswirar karkashin teku ta yankin da za a yi aikin.

Haka kuma wani jirgin ruwan Holland Sonar gondola, wanda ke cikin aikin yana da kayayyakin aiki na zamani.

Jirgin ya kammala bincike a kudancin tekun India, inda masu bincike suke ganin jirgin na Malaysia ya fadi.

Aikin taswirar da ake dauka yanzu dai, ta yankin tekun da za a yi aikin, shi ne irinsa na farko a yankin da babu wata masaniya a kansa sosai.

Idan ba a samar da wannan taswirar ba, wadda ta kai ta zurfin akalla mita 25 a bangaren tekun da ya fi zurfi, akwai hadari a sanya na'urorin aikin a karkashin tekun saboda za su iya bacewa.

Yanki mafi zurfi da aka sanya na'urorin ya zuwa yanzu shi ne na mita 13.